An harbe kanin dan wasan Tottenham, Serge Aurier a Faransa

Asalin hoton, Reuters
An harbe kanin dan wasan Tottenham, Serge Aurier a birnin Toulouse da ke Faransa a kofar gidan rawa in ji wasu rahotanni.
Christopher Aurier ya mutu a asibiti sakamakon harbinsa a ciki da aka yi, kamar yadda wasu jaridun Faransa suka wallafa.
Sai dai wanda ya kashe shin ya bar wurin cikin sauri ba wanda zai iya shaida shi kamar yadda wadanda suka je wurin suka sanar.
Christopher Aurier, wanda dan kasar Ivory Coast ne kamar yayansa yana taka leda ne a Faransa.
Mai shekara 26 yana taka leda a karamar kungiya Rodeo da ke Toulouse mai buga karamar gasar Faransa ta biyar a bara.
Ya kuma buga Racing Club de Lens da Gueugnon, Chantilly da kungiyar Belgium Rebecq, Le Figaro.
Yayansa, Serge mai shekara, 27, shi ne kyaftin din tawagar Ivory Coast wanda ke taka leda a Tottenham.























