Saudi Arabia ta hana beIN Sport gabatar da shirye-shirye a kasar

A general action shot from Newcastle v West Ham at St James' Park
An wallafa

audi Arabia ta hana beIN Sport, wacce take da ikon tallata gasar Premier League a gabas ta tskiya daga gabatar da shirye-shiryenta a kasar.

Hakan na nufin kasar ba za ta kalli wasannin gasar Premier League ba, duk da shirin da take na kokarin sayen Newcastle United.

Mahukuntan gasar Premier League ake ta jiran amincewa da tayin fam miliyan 300 kudin sayen kungiyar da aka yi.

Gwamnatin Saudia Arabia ta ce ''kamfanin watsa shirye-shiryen wasannin ya karya ka'idojin da ta gindaya masa a lokacin da ke gudanar da aiki a karo da dama''.

Lauyoyin Premier League na yin nazarin sayar da Newcastle United ga Saudi Arabia tsawon wata uku.

Gwamnatin Burtaniya ta bukaci a hana kasar sayen Newcastle da Saudi Arabia za ta biya kaso 80 cikin 100 - har sai an binciki kasar kan zargin satar fasahar talabijin.

Kamfanin beIN Sports ne keda alhakin nuna wasannin Premier League a gabas ta tsakiya, wanda ya biya fam miliyan 400 kan kwantiragin shekara uku.

A watan Yuni cibiyar kasuwanci ta duniya ta ce Saudi Arabia ta karya dokar satar fasaha da ta shafi beoutQ, wacce ake zargin tana nuna fitattun wasanni ciki har da gasar Premier League.

Saudi Arabia ta sha musanta cewar hannunta a beoutQ gudanar da ayyukan da take yi - ta kara da cewar ba ta da wata alaka da kamfani da ta kai karya ka'idar satar fasahar talabijin.