Makomar Sancho, Costa, Jimenez, Ceballos, Harrison da Aubameyang

Jadon Sancho
An wallafa

Dan wasan gaba naBorussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, sai ya nema wa kansa mafitar komawa Manchester United ta hanyar nuna wa kulub dinsa na Jamus cewa zai tafi. (Mirror)

Juventus na son haifar da hamayya tsakanin da Manchester City da Paris St-Germain kan dan wasan Brazil Douglas Costa, mai shekara 29, wanda take son maye gurginsa da dan wasan Wolves da Mexico Raul Jimenez, mai shekara 29. (Tuttosport)

Dan wasan tsakiya na Arsenal da Spain Dani Ceballos, mai shekara 23 yana son Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya amince ya tsawaita zamansa tare da Gunners har zuwa karshen kaka mai zuwa. (El Confidencial, via Express)

Kungiyar Leeds United da ta tsallako gasar Premier ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da rike dan wasan gaba na Manchester Cityna Ingila Jack Harrison, mai shekara 23, a matsayin dan wasan aro har zuwa badi. (Manchester Evening News)

Matashin dan wasan tsakiya na West Hammai shekara 16 Benicio Baker-Boaitey yana shirin komawa Bayern Munich kuma zai tafi Jamus domin kulla yarjejeniya. (Sun)

Dan wasan tsakiya na Brazil Willian, mai shekara 31 da ake alakantawa da Tottenham, Arsenal da Manchester United - ya bayyana cewa jiran tsammani a Chelsea kan sabuwar yarjejeniya bayan ya nemi a kwangilar shekara uku amma aka ma shi tayin shekara biyu. (De Sola, via Mirror)

KocinNewcastle Steve Bruce za a datse yawan kudin da aka ware masa domin zubin sabbin 'yan wasa saboda kudaden shigar kulub din £170m a bara za su yi kasa bisa dalilai da suka hada da har da maido da kudaden tikiti da kuma . (Mirror)

Yadda dan wasan baya na Brazil David Luiz, mai shekara 33, ya sauya zai iya canza tunanin Mikel Arteta inda kocin na Arsenal ke shirin cefanen 'yan wasa. (Star)

Manchester United ta ba Jude Bellingham da iyayensa damar kawo ziyara filinta na atisaye kuma a gaban idon Sir Alex Ferguson a wani yunkuri na yanyo ra'ayin dan wasan mai shekara 17 na Birmingham ya amince ta saye shi amma kuma ya zabiBorussia Dortmund.(Mail)