Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Bale, Sancho, Grealish, Havertz, Pereira, White, Traore

Asalin hoton, Getty Images
Jose Mourinho yana son ya dawo da dan wasan Real Madrid da Wales Gareth Bale, mai shekara 31, Tottenham. (Cuatro - in Spanish)
An bai waChelsea dan wasanParis St-Germain da Brazil Thiago Silva, mai shekara 35, wanda zai bar kungiyar ta Faransa bayan wasan karshe na Gasar Zakarun Turai. (Telegraph)
Rashin cimma matsaya ya jinkirta shirin Manchester United na dauko dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila mai shekara 20, Jadon Sancho. (ESPN)
Mai yiwuwa Manchester United ta ba da golanta dan kasar Argentina Sergio Romero, mai shekara 33, ga Aston Villa a wani bangare na yarjejeniyar dauko dan wasan Ingila mai shekara 24, Jack Grealish. (Mail)
Chelsea za ta kammala dauko dan wasan Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, a kan kwangilar shekara biyar a makon nan idan ita da Bayer Leverkusen za su iya rage bambancin £18m kan farashin dan wasan. (Telegraph)
Chelsea da Atletico Madrid suna son dauko dan wasan Juventus da Italiya mai shekara 26 Federico Bernardeschi. (Calciomercato - in Italian)
Benfica da Valenciasuna son dauko dan wasanManchester United da Brazil Andreas Pereira, mai shekara 24. (ESPN)
United ta dawo da shirinta na zawarcin dan wasan Juventus da Brazil Alex Sandro, mai shekara 29. (Calciomercato - in Italian)
A karo na ukuLeeds ta nemi daukodan wasan Brighton dan kasar Ingila Ben White - kuma an yi amanna ta ware kusan £25m don dauko dan wasan mai shekara 22. (Sky Sports)
Wolves ta shirya domin sayar da dan wasan Sufaniya Adama Traore a farashin mai gwaɓi duk da yake saura shekara uku kwangilar dan wasan mai shekara 24 ta kare. (Mail)
Liverpool na shirin sayar da dan wasan tsakiyar Serbia Marko Grujic, mai shekara 24, da dan wasan Wales Harry Wilson, mai shekara 23, a bazarar nan. (Mirror)
Tottenham tana son aron dan wasan Liverpool dan kasar Ingila mai shekara 21 Rhian Brewster. (Football Insider)
West Ham tana son sayar da dan wasan Ingila Jordan Hugill, mai shekara 28, a bazarar nan. Hugill ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a QPR. (Evening Standard)



























