Rahoton kungiyar Kick It Out ya ce an samu karin ne a 2019-20

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Kick It Out ta saki rahoton karuwar nuna wariya a kwallon kafar Ingila da kashi 40 cikin 100 a kakar da ta gabata, wanda aka bayyana shi a matsayin abin tsoro.
Kungiyar dake yaƙi da nuna wariyar ta ce rahoton da ta samu ya nuna wariyar ta karu daga 313 a 2028-19 zuwa 446 a 2019-2020 duk da cewa an buga wasanni ba tare da 'yan kallo ba.
Rahoton nuna wariyar launin fata a manyan wasanni ya karu zuwa kashi 53 cikin 100, yayin da aka samu nuna wariyar jinsi da kashi 95 cikin 100.
Bayanai sun nuna an samu karuwar yadda ake harar 'yan wasa a kafafan sada zumunta ta bangaren nuna wariyar launin fata da kashi 71 cikin dari.
Bayanan da wata kungiya ta YouGov ta samu daga magoya baya 1,000 wanda Kick It Out ta wallafa, sun ta jin maganganun nuna wariyar launin fata lokacin da ake ihu a yayin wasanni.
Sanjay Bhandari shi ne shugaban kungiyar ya kuma ce kwallon kafa ta bi matsalar korona yadda ya dace da kuma mutuwar George Floyd a Amurka a watan Mayu, wadda ta janyo zanga-zanga a duniya.
Ya ƙara da cewa "Sai dai a bayan fage, ƙiyayya da banbanci tsakanin al'umma ma ci gaba da zama wata babbar barazana.
"Rahotonmu ya nuna 'yadda nuna wariya ke kara habbaka cikin shekara biyu da ta gabata, wanda ke nuna alkaluman nuna wariya da manyan laifuka na karuwa a fadin kasar cikin shekaru hudu baya."
An dakatar da wasan kwallon kafa a watan Maris saboda annobar korona, har da gasar Premier da Championship da aka dawo ba tare da magoya baya ba a fili.
An ta samun matsaloli a kafafen sadarwa na intanet kan nuna wariyar launin fata, kamar wanda aka yi wa dan wasan Crystal Palace da kuma dan wasan gaba na Sheffield United David McGoldrick.
Bhandari ya ce"Kafafen sada zumunta sun zama wani filin yaki tare da yaɗa kiyayya da nuna banbanci. yana da kyau mu hada hannu tare wajen cimma nasarar wannan yaki.
"Muna bukatar dokoki na musamman da hada hannu da kamfanonin sa da zumunta domin neman mafita."



























