West Ham: David Moyes da Issa Diop da Josh Cullen sun kamu da cutar korona

David Moyes on the touchline
An wallafa

Kocin West Ham United, David Moyes da 'yan wasan kungiyar biyu sun kamu da cutar korona.

An sanar da mahukuntan gasar Premier League halin da ake ciki a lokacin da kungiyar ke shirin buga Carabao Cup da Hull City ranar Talata a London Stadium.

Moyes, mai shekara 57, da mai tsaron baya Issa Diop, mai shekara 23, da kuma mai shekara 24 mai buga wasan tsakiya Josh Cullen za su killace kansu.

"Kocin da 'yan wasan biyu sun bar West Ham United sun koma gida nan take," a wani jawabi da kungiyar da sanar.

West Ham ta ce tun farko mutanen uku ba su nuna suna dauke da annobar ba, kuma mataimakin koci, Alan Irvine shi ne zai ja ragamar karawa da Hull a wasan da aka tsara Diop da Cullen za su buga.

Dokar gwamnatin Ingila ta bukaci duk wanda ya kamu da cutar korona ya killace kansa na kwana 10, hakan na nufin Moyes da Diop da kuma Cullen ba za su halaci atisaye tare da 'yan wasa ba.

Haka kuma ba za su buga gasar Premier League da West Ham za ta fafata da Wolverhampton Wanderers ranar 27 ga watan Satumba ba.

Wannan lamarin ya faru ne a lokacin da aka soke wasan Leyton Orient da Tottenham a gasar Caraboa Cup ranar Talata, bayan da aka samu 'yan kwallo da yawa dauke da cutar korona.