Andreas Pereira: Man Utd za ta bai wa Lazio aron Pereira

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Manchester United ta amince ta bayar da aron Andreas Pereira ga Lazio zuwa karshen kakar bana ta tamaula.
Mai shekara 24 ya koma taka leda a Old Trafford tun 2014.
Kafin nan dan kwallon ya buga wasannin aro a gasar La Liga ta Spaniya a kungiyar Granada da kuma Valencia.
Dan wasan ya kusan karbar gurbi a Old Trafford a kakar da ta wuce, inda ya buga karawa 40 a dukkan fafatawa.
Tun lokacin da Bruno Fernandes ya fara buga wa United tamauala, Pereira ya yi wasa daya kacal da canji shida.
Fernandes ya fara yi wa United wasa ranar 1 ga watan Fabrairu a gumurzu da Wolverhampton.























