Burnley 0-3 Manchester City: Raheem Sterling ne ya ci kwallo biyu a Carabao Cup

Asalin hoton, Rex Features
A karon farko Raheem Sterling ya ci wa City kwallo a kakar bana, inda ya fara da biyu, yayin da Ferran Torres shi ma a karon farko ya ci wa kungiyar kwallo. bana.
Manchester City ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe a Caraboa Cup, bayan da ta yi nasarar doke Burnley da ci 3-0 ranar Laraba.
City ce ta mamaye wasan daga nan ne Sterling ya ci kwallo, bayan da Benjamin Mendy ya taimaka masa.
Ta biyun kuwa daga kusa Sterling ya ci bayan kwallon da Torres ya buga masa, dan wasan da ya koma Etihad a cikin watan Agusta daga Valencia kan fam miliyan 20.78
Wannan nasarar za ta karfafa gwiwar kungiyar ta Pep Guardiola wanda Leicester City ta doke da ci 5-2 a gasar Premier League ranar Lahadi.
Ranar Alhamis za a raba jadawalin daf da na kusa da na karshe a Caraboa idan an kammala wasan Liverpool da Arsenal.























