An wanke dan wasan Marseille, Alvaro Gonzalez wanda Neymar ya ce ya yi masa kalaman wariya

Paris St-Germain forward Neymar
An wallafa

Hukumar kwallon kafar Faransa ta wanke dan wasan Marseille, Alvaro Gonzalez wanda Neymar ya zarga da cewar ya yi masa kalaman wariya.

An bai wa Neymar jan kati, bayan da ya doki Gonzalez a karawar da Paris St Germain ta yi da Marseille a gasar Lique 1 ranar 13 ga watan Satumba.

A kafar sada zumunta Neymar ya yi zargin cewar mai tsaron bayan ya yi masa kalaman wariya.

Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta ce ba ta samu wata kwakkwarar shaida da za ta dogara da ita wajen yanke hukunci ba.

Neymar ne dan kwallo na biyar da aka bai wa jan kati a karawar da PSG a gasar ta Lique 1.