Xherdan Shaqiri: Dan wasan Liverpool ya kamu da cutar korona

Xherdan Shaqiri
Bayanan hoto, Xherdan Shaqiri ya ci kwallo a wasa daya da ya buga wa Liverpool a bana a 7-2 da ta doke Lincoln City
An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Switzerland ta ce dan wasan Liverpool, Xherdan Shaqiri ya kamu da cutar korona.

Shaqiri mai shekara 26 ya je kasarsa domin buga mata wasa amma yanzu ya killace kansa.

Shi ne dan kwallon Liverpool na uku da ya kamu da annobar bayan Thiago Alcantara da kuma Sadio Mane.

Wasa daya tal Shaqiri ya buga wa Liverpool a kakar bana, shi ne ranar 24 ga watan Satumba a karawa da Lincoln a Caraboa Cup. Bai sake buga Premier League ba a shekarar nan.

A gasar Switzerland, mutane za su killace kansu kwana 10 tun daga ranar da alamun cutar suka bayyana.

Switzerland za ta buga wasan sada zumunta da Croatia ranar Laraba sannan ta buga gasar Nations League da Spain ranar 10 ga watan Oktoba, kwana uku bayan haka kuma ta fafata da Jamus.