Edinson Cavani: Sabon ɗan ƙwallon Manchester United ba zai fara wasa da wuri ba

Asalin hoton, Getty Images
Sabon dan kwallon da Manchester United ta dauka Edinson Cavani zai dan jira kafin ya fara buga mata tamaula, saboda dokar killace kai don hana yada cutar korona.
Dan wasan tawagar Uruguay, ya koma United ranar Litinin, bayan da kwantiraginsa ya kare a Paris St Germain.
Cavani, mai shekara 33, zai shiga kwanakin killace kai na mako biyu, bayan da ya isa Ingila daga Faransa ranar Lahadi
United za ta buga wasan gaba na Premier League ranar 17 ga watan Oktoba, inda za ta ziyarci Newcastle United.
Hakan na nufin kocin United, Ole Gunnar Solskjaer zai je St James Park ba tare da Anthony Martial, wanda aka bai wa jan kati a wasa da Tottenham ranar Lahadi.
Cavani bai yi atisaye da 'yan wasan United ba har sai an shawo kan lamarin, ba zai kuma buga Champions League da kungiyar ta Old Trafford za ta ziyarci PSG a karawar rukuni ba ranar 20 ga watan Oktoba.
A cikin watan Agusta sai da dan kwallon tawagar Ingila, Harry Kane ya killace kansa mako biyu kan ya fara wasanni, bayan da ya je hutu a Barbados.























