Damben gasa : Turmi biyu aka yi ba kisa tsakanin Shagon Nura da Dan Sama'ila

Damben gasa na matasa tsakanin Shagon Nuran Dogon Sani da Ɗan Sama'ila sun tashi ba kisa bayan turmi biyu da suka fafata ranar Lahadi a Abuja.
Tun farko, Ali Zuma ne ya sa musu ladan naira 60,000 a tsakaninsu ga duk wanda ya yi nasara a damben.
Kamar yadda lissafi ya kama duk wanda ya buge zai karbi naira 30,000 duk wanda ya fadi yana da naira 20,000 a bai wa makada naira 10,000.
Tun kan a fara wasan a DeiDei da ke Abuja, Ali Zuma ya sanar cewar ko turmi biyu suka yi mai kyau ya wadatar, idan ta yi kisa shikenan, idan ba ta yi ba zai raba wasan.
Shagon Nuran Dogon Sani daga Arewa da Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu sun sami alheri tun kan su taka dambe, inda masoya suka dunga yi musu ruwan kudi.

Bayan da fili ya natsa ne suka fara dambe a tsakaninsu, koda yake Shagon Nura bai tashi ba a koda yaushe Bahagon Dan Sama'ila ne ya dunga kai hare-hare.
Bayan turmin farko ba kisa a na biyu an ci karo da taƙaddama, inda Shagon Nura ya hankaɗe Bahagon Sama'ila daf da fili, koda yake ya yi ta maza ya kama igiya da taimakon buhu da turke bai je kasa ba.
'Yan kallo sun fara hayaniya cewar Bahagon Ɗan Sama'ila ya je kasa, sai dai Ali Zuma ya raba gardama, inda ya bukaci su ci gaba da wasa ba kisa.
Haka suka yi turmi na biyu damben bai yi kisa ba, an kuma biya 'yan kallo har ma ake sa ran watakila mako mai zuwa a kara hadasu da kudi mai tsoka.
Wasu wasannin da aka buga.
- Shagon Faya da Na Dan Jamilu.
- Guguwar Mai Takwasara da Shagon Autan Faya
- Dan Katsinawa da Shagon Soja
- Shagon Ali Kanin Bello da Taufik Dogon Ebola



























