Premier League: Mutum biyar sun kamu da cutar korona a gwaji 1,128 da aka yi

A testing station in the Premier League
Bayanan hoto, An samu karancin mutanen da suka kamu da annobar fiye da gwaje-gwajen da aka yi a baya
An wallafa

Premier League ta tabbatar cewar mutum biyar na dauke da cutar corona, bayan wani gwaji da ta gudanar kwanan nan.

An gwada jami'ai da 'yan wasa 1,128 tsakanin Litinin 5 ga watan Oktoba zuwa Lahadi 11 ga watan.

Wadanda suka kamu da annobar an bukaci su killace kansu kwana 10 daga nan a sake gwada su kafin su koma hulda da mutane.

Mutum tara aka samu dauke da cutar tsakanin 28 ga watan Satumba zuwa 4 ga watan Oktoba, bayan da aka samu mutum 10 kwana bakwai kafin gwajin na daga 28 ga Satumbar.