Peru 2-4 Brazil: Neymar ne na biyu a yawan cin kwallo a tawagar Brazil

Neymar
Bayanan hoto, Dan wasan Paris St-Germain, Neymar ya ci tawagar Brazil kwallo 64
An wallafa

Neymar na biye da Pele a jerin wadanda ke gaba a ci wa tawagar Brazil kwallaye, bayan da ya ci Peru uku rigis a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2022.

Dan wasan Paris St-Germain ya ci wa Brazil kwallo 64 jumulla, bayan nasara da ci 4-2 da ta yi.

Sau biyu Peru ke fara cin kwallo Brazil na farkewa a karawar da suka yi a Lima, yayin da Neymar ya ci biyu da fenariti da hakan ya dara Ronaldo a ci wa Brazil kwallaye, Pele ke mataki na daya da 77.

Dan wasan Everton, Richarlison shi ma ya ci kwallo da ka, bayan da Roberto Firminio ya buga masa tamaular.

Neymar, mai shekara 28, ya ci kwallayen ne a wasa 104 da ya buga wa tawagar Brazil, yayin da Pele ya yi karawa 92.

Brazil da Argentina na kan gaba a kan rukunin, bayan da suka ci wasanninsu bibiyu, yayin da Paraguay wacce ta doke Venezuela 1-0 ranar Talata tana mataki na uku.

Duk kasashen da suka karkare daga mataki na daya zuwa hudu a rukuni za su je gasar kofin duniya kai tsaye a Qatar a 2020, yayin da ta biyar za ta buga karawar cike gurbi.