Said Benrahma: West Ham ta kusan daukar dan kwallon Brentford

Said Benrahma scores for Brentford against Fulham
An wallafa

West Ham na daf da kammala daukar dan wasan Brentford, Said Benrahma kan fam miliyan 30 kafin ranar Juma'a da za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Ingila.

An fahimci cewar West Ham ta amince ta fara biyan fam miliyan 25 daga baya ta cika fam miliyan biyar kudin tsarabe-tsarabe.

Ranar Laraba dan kwallon mai shekara 25 ya koma Ingila, bayan da ya buga wa tawagar Algeiya tamaula, ana kuma sa ran shi ne zai maye gurbin Felipe Anderson a West Ham din.

Ana sa ran zai je a auna koshin lafiyarsa a ranar Alhamis, kafin ya rattaba hannu kan kwantiragi.

Benrahma, ya ci wa Brentford kwallo 17 a wasa 43 da ya buga a gasar Championship a bara.

Brentford wacce ta dauki Benrahma daga Nice kaka biyu da ta wuce, ta ci riba mai tsoka da ta sayar da shi ga West Ham United.

Tun daga 5 ga watan Oktoba aka amince kungiyoyin Premier League su yi ciniki tsakaninsu da masu buga gasar Championship da League One da League two a Ingila zuwa 16 ga watan na Oktoba.