Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Haaland, Kane, Traore, Xhaka, Linglet da Zappacosta

Jaridar Telegraph ta ruwaito cewa Manchester City na shirin gabatar da sabon ta yi kan ɗan wasan Tottenham Harry Kane.
Sai a wannan makon kyaftin ɗin na Ingila ya buga wa Tottenham wasa, a lokacin da aka saka shi bayan dawowa hutun rabin lokaci a wasan da suka doke Wolves har gida.
A wata mai kama da haka Tottenham na shirin taya ɗan wasan gaban Wolves din Adama Traore kan fam miliyan 40 in ji Telegraph.
Manchester United ta samu ƙwarin gwuiwa kan neman da ta ke yi wa ɗan wasan gaban Borussia Dortmund Erling Haaland mai shekaru 21.
Kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito, Dortmund ta saka fam miliyan 64 ga duk wanda ke son warware kwantiragin ɗan wasan kafin watan Janairun 2022.
Arsenal ta gaza sayen ɗan wasan Italiya da Sassuolo wato Manuel Locatelli.
Duk da Arsenal ta fi tayi mai tsoka, jaridar Gazzeta di Modena ta ruwaito cewa ɗan wasan ya zaɓi tafiya Juventus kan Arsenal.
A wata mai kama da haka mamallakin Arsenal Stan Kroenke ya bayyana cewa Granit Xhaka ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya a ƙungiyar.
Ita kuwa Sky Sport ta ce mai tsaron bayan Chelsea da Italiya Davide Zappacosta ya shirya kammala zuwa Atalanta.
Har wa yau Roma ta nuna sha'awar sayen mai tsaron bayan Barcelona Clement Lenglet kafin a rufe kasuwa inji Corriere dello Sport.



























