Arsenal 0-2 Chelsea: Gunners tana wani hali mai wahala in ji Mikel Arteta

Mikel Arteta
An wallafa

Arsenal tana ''mawuyacin halin da ba ta saba da shi ba'' bayan da ta fara kakar Premier League ta bana da kafar hagu in ji Mikel Arteta.

Arsenal ta yi rashin nasara da ci 2-0 a gidan Brentford a wasan makon farko a gasar bana, sai Chelsea itama ta ci Gunners 2-0 a karawar mako na biyu.

Kungiyar ta Emirtaes ta yi wasa biyu a jere da rashin nasara, kuma ba ta zura kwallo ba a raga da fara Premier League ta 2021-22.

'Yan wasan Arsenal sun ci karo da koma bayan cutar korana, wadda ta kama wasu daga ciki daf da za a fara wasannin bana.

''Bana jin a tarihin kungiyar nan ta taba cin karo da wani abu kamar haka'' kamar yadda Arteta ya sanar da BBC.

''Za mu fuskanci kalubalen nan, kuma ba a watan Agusta ake bai wa zakara kofin Premier League ba. Abin kunya da za ka yi shine ka sare daga wasannin, mu kuma hakan ba zai yiwuba.''

Chelsea ta ci Arsenal kwallaye biyun ta hannun Romelu Lukaku - a wasan farko da ya buga wa kungiyar da ta dauke shi fam miliyan 97.5 a bana, sannan Reece James ya kara na biyu.

Arsenal tana cikin 'yan ukun karshe a teburin Premier League a kakar nan tun daga wasan farko da na biyu a karon farko tun bayan 1992.

Arteta ya kara da cewar ''Ya kamata a fuskanci halin da muka tsinci kan mu. Mun yi rashin fitattun 'yan wasanmu tara, lamari ne mai wuyar sha'ani.''

Arsenal ta buga fafatawar biyu ba tare da fitattun 'yan wasanta Pierre-Emerick Aubameyang da Alexandre Lacazette - har da Willian da mai tsaron raga Alex Runarsson, wadanda suka killace kan su saboda cutar korona.

Aubameyang ya yi zaman benci a karawa da Chelsea ranar Asabar, amma dan kwallon da ta dauka a bana kan fam miliyan 50, Ben White ya killace kansa, bayan da ya kamu da cutar korona.

Dan wasa Thomas Partey da Gabriel da kuma Eddie Nketiah na yin jinya.

Magoya bayan Arsenal sun yi ta yi wa kungiyar kuwa a karon farko da suka shiga Emirates kallon tamaula, tun bayan kawan 533 - sai dai Arteta bai damu da ihun ba.