Federico Valverde: Dan kwallon Uruguay zai ci gaba da wasa a Real Madrid

Federico Valverde
An wallafa

Federico Valverde ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Real Madrid zuwa karshen kakar 2027.

Tun farko kwantiragin dan wasan mai shekara 23, dan kwallon tawagar Uruguay zai kare a karshen watan Yunin 2025.

Cikin kunshin yarjejeniyar da ya amince a bana ta kaka biyu har da karin kudi da ya kai fam miliyan 1.17.

Valverde ya koma Madrid daga wata kungiyar Uruguayan, club Penarol a cikin watan Yulin 2016, ya kuma fara taka leda daga karamar kungiyar.

Ya je aro a Deportivo La Coruna a 2017-18, daga baya ya koma Real Madrid wadda ya fara buga wa tamaula karkashin Santi Solari.

Valverde ya lashe kofin LaLiga a kakar 2019-20 karkashin Zinedine Zidane, wanda ya saka shi wasa 21 a lokacin.

Dan kwallon ya yi wa Real fafatawa 24 a gasar La Liga a bara, wanda ya ci kwallo uku a raga.

Mai buga wasa daga tsakiya ya zama na farko da ya tsawaita yarjejeniyar sa a Real Madrid, tun bayan da Carlo Ancelotti ya karbi kungiyar cikin watan Yuni.

Wadanda suka tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a Real Madrid a bana sun hada da Luka Modric da Nacho Fernandez da Karim Benzema da Dani Carvajal da kuma Thibaut Courtois.

Real Madrid ta doke Deportivo Alaves a wasan makon farko a La Liga, sannan ta tashi 3-3 a gidan Levante a wasa na biyu a gasar ta Sifaniya ranar Lahadi.