Lucas Torreira: Fiorentina ta dauki aron dan wasan Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Dan wasan Arsenal, Lucas Torreira ya kammala komwa Fiorentina, wadda zai buga wa tamaula aro zuwa karshen kakar bana.
Fiorentina tana da zabin mallakar dan kwallon, mai shekara 25, bayan kammala kakar bana, idan ya taka rawar gani.
Torreira ya buga wa Arsenal karawa 89, tun bayan da ya koma kungiyar daga Sampdoria a 2018, yana cikin 'yan wasan Gunners da suka lashe FA Cup a 2020.
Ya buga wasannin aro a kakar bara a Atletico Madrid, wadda ya yi wa karawa 26 a dukkan fafatawa a kungiyar.























