Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Damsgaard, Mbappe, Kounde, Vlasic, Icardi, Sabitzer

Damsgaard
An wallafa

WatakilaLiverpool, Leeds da Aston Villa su nemi daukar dan wasan Sampdoria da Denmark Mikkel Damsgaard, sai dai Tottenham ta daina zawarcin dan wasan mai shekara 21, wanda ya murza wa kasarsa leda a gasar Euro 2020. (La Repubblica via Sport Witness)

Har yanzu Paris St-Germain ba ta bayar da amsa ga bukatar Real Madrid ta daukar dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22 ba, yayin da kungiyar ta La Liga ta ware ranar Litinin a matsayin wa'adi na karshe ga kungiyar da ke murza Ligue 1 kan ko ta amince ko kuma ta ki amincewa da tayinsu. (Marca)

Sevilla ba za ta amince da kasa da euro 80m (£68.5m) kan dan waan Faransa Jules Kounde ba. Ana rade radin Chelsea za ta nemi daukar dan wasan mai shekara 22 bayan sayar da Kurt Zouma, mai shekara 26, ga West Ham. (Marca - in Spanish)

West Ham na dab da kammala biyan £25m domin daukar dan kasar Croatia Nikola Vlasic, mai shekara 23, daga CSKA Moscow. (Guardian)

Aston Villa na shirin bayar da £15m domin daukar dan wasan Liverpool da Ingila Curtis Jones, mai shekara 20, wanda har yanzu bai buga wa the Reds a kakar bana ba. (Sun)

Everton, Brighton, Leeds da Crystal Palace suna fafatawa domin daukar dan wasan Manchester United da Wales Daniel James, mai shekara 23, wanda aka amince ya bar Old Trafford yayin da dan wasan Portugal mai shekara 36 Cristiano Ronaldo yake shirin komawa United daga Juventus. (Star)

Everton tana tattaunawa domin daukar dan wasan Venezuela Salomon Rondon daga kungiyar kasar China Dalian Professional. Kocin Everton Rafael Benitez ya taba jagorantar dan wasan mai shekara 31 a China da Newcastle. (Sky Sports)

Watford tana tattaunawa da Birmingham game da sayar da dan wasa mai shekara 33 wanda shi ne kyaftin na kungiyar Troy Deeney. (Athletic - subscription required)

Juventus za ta nemi daukar dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Belgium Axel Witsel, mai shekara 32, yayin da Massimiliano Allegri yake son inganta tsakiyarsa. (Sky Sport - in Italian)