Jordan Henderson: Kyaftin din Liverpool zai ci gaba da wasa a kungiyar

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin din Liverpool, Jordan Henderson ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa karshen kakar 2025.
Mai shekara 31, dan kwallon tawagar Ingila ya yi wa Liverpool wasa 394, kuma sauran kaka biyu kwantiragin sa ya kare a Anfield.
Henderson shine na baya-bayan nan da ya ci Champions League da kuma Premier League ya tsawaita yarjejeniyar sa a Liverpool, bayan Fabinho da kuma Andy Robertson.
Wanda ya koma Anfield daga Sunderland a 2011, Henderson ya lashe kofi biyar a Liverpool, inda ya fara da cin League Cup karkashin koci, Kenny Dalglish a shekarar 2012.
A matsayin sa na kyaftin din kungiayar ya daga kofin Premier League da Champions League da Uefa Super Cup da kuma Fifa Club World Cup trophies.
Kwazon da ya sa a lokacin da Liverpool ta dauki Premier a karon farko, bayan shekara 30 ya sa kungiyar marubuta labarin wasanni ta bashi kyautar gwarzon dan kwallon kafa na 2020.























