Hector Bellerin: Arsenal za ta bai wa Real Betis aron dan wasan

Hector Bellerin
Bayanan hoto, Bellerin ya koma Arsenal daga karamar kungiyar Barcelona a 2011
An wallafa

Mai tsaron bayan Arsenal daga hagu, Hector Bellerin na daf da komawa aro ga Real Betis mai buga gasar La Liga.

Mai shekara 26 dan kasar Sifaniya, za a auna koshin lafiyar dan wasan a Landan ranar Talata.

Bellerin baya buga wa Gunners wasanni da yawa, tun bayan da ya yi mummunan rauni a 2019. amma ya buga karawa 25 a Premier League a bara.

Dan kwallon bai yi wasa ba a kakar bana ba, wanda keda sauran shekara biyu yarjejeniyar sa ta kare a kungiyar.

Arsenal ta dauki Bellerin daga karamar kungiyar Barcelona a 2011.

Ya kuma yi wa Gunners karawa 239 da cin kwallo tara.

Calum Chambers da kuma Cedric Soares ne suka tsare bayan Arsenal daga hagu a wasa uku a Premier League da kungiyar ta yi rashin nasara a jere a bana.

Arsenal ta dauki 'yan kwallo da yawa a bana ciki har da Ben White kan fam miliyan 50 da Martin Odegaard kan fam miliyan 30 mai tsaron raga Aaron Ramsdale kan fam miliyan 24.