Eduardo Camavinga: Real Madrid ta dauki dan wasan Faransa daga Rennes

Camavinga became the youngest France international since 1914 last year
Bayanan hoto, Camavinga ya zama matashin dan kwallon tawagar Faransa a karon farko tun bayan 1914
An wallafa

Real Madrid ta kammala daukar dan kwallon tawagar Faransa, Eduardo Camavinga daga Rennes kan yarjejeniyar kaka biyar.

Mai shekara 18 yana cikin kwantiragin karshe a kungiyar da ke buga Ligue 1, wadda ta sayar da shi in ba haka ba zai yi zaman mara yarjejeniya da kungiyar.

Ranar Litinin aka auna koshin lafiyar dan kwallo a Faransa a wajen atisaye na Clairefontaine.

A watan Afirilun 2019, Camavinga ya zama matashin dan wasan Rennes da ya fara taka mata leda yana da shekara 16 da haihuwa da wata hudu a lokacin.

Cikin kaka biyun da ya yi a kungiyar ya buga mata karawa 60.

Matashin ya zama mai karancin shekaru da ya buga wa tawagar Faransa tamaula a karawa da Croatia a Nations League a Satumbar 2020.

Ya kuma fara ci wa Faransa tamaula wata daya tsakani a wasan sada zumunta da Ukraine da ta yi nasara da ci 7-1.

Bayan da Faransa ba ta gayyace shi Euro 2020, ya wakilci kasar a gasar cin kofin nahiyar Turai ta matasa 'yan kasa da shekara 21 a bana.

Camavinga shine na biyu da Real Madrid ta dauka, bayan David Alaba, wanda ya koma Sifaniya da taka leda daga Bayern Munich.

Ana ta alakanta Real Madrid da cewar za ta dauki Kylian Mbappe daga Paris St-Germain, sai dai har yanzu kungiyoyin biyu ba su kai ga kulla yarjejeniya ba.