Dan kwallon Real Madrid Luca Modric ya yi bikin cika shekara 36

Asalin hoton, Real Madrid FC
An wallafa
Dan wasan tawagar Croatia, mai taka leda a Real Madrid, Luca Modric ya yi bikin cika shekara 36 ranar Alhamis.
An haifi dan kwallon a Zadar da ke Crotia ranar 9 ga watan Satumbar 1985.
Kawo yanzu ya buga wa Real karawa 392 ya kuma lashe kofi 17 a kungiyar ta Sifaniya.
Ya kuma koma Real Madrid a kakar 2012/13, wanda ya lashe Champions League hudu da Club World Cup hudu da European Super Cup uku da LaLiga biyu da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup uku.
Dan kwallon ya lashe kyautar dan wasan da ba kamar sa a duniya ta FIFA da ta Ballon d'Or.
Cikin wasa 392 da ya yi wa Real Madrid ya kuma ci mata kwallaye 28.























