Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga a bana

Robert Lewandowski
An wallafa

Ranar Lahadi za a karkare wasannin mako na hudu a gasar Bundesliga, wadda tuni aka samu 'yan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye.

Robert Lewandowski ne ya zama na daya a yawan cin kwallaye a gasar Bundesliga a bara mai 41. Shin ko a kakar bana zai ci gaba da jan ragama ko kuma Erling Haaland ko Andre Silva ko kuma wani da ba a yi tsammani ba.

Robert Lewandowski

Kungiya: Bayern Munich

Shekarar haihuwa: 33

Wasannin da ya buga: 4

Kwallon da ya ci: 6

A sabuwar kakar bana ta 2021/22 Lewandowski ya ci kwallo a karawar mako na daya da na biyu ya kuma ci uku rigis a wasan mako na uku a fafatawa da Hertha Berlin, hakan ya yi bajintar cin kwallo a wasa 16 a jere a kungiyar.

Haka kuma Lewandoeski ya kara zura kwallo a ragar RB Leipzig a wasan mako na hudu da ta ci 4-1 ranar Asabar.

Wadanda ke kan gaba a cin kwallo a Bundesliga ta bana:

  • Robert Lewandowski FC Bayern Munich kwallo 6
  • Erling Haaland Borussia Dortmund kwallo 5
  • Taiwo Awoniyi FC Union Berlin kwallo 3
  • Anthony Modeste FC Koln kwallo 3
  • Moussa Diaby Bayer 04 Leverkusen kwallo3
  • Patrik Schick Bayer 04 Leverkusen kwallo3

Wasannin mako na biyar a gasar Bundesliga:

Juma'a 17 ga watan Satumba

  • Hertha BSC da SpVgg Greuther Furth

Asabar 18 ga watan Satumba

  • DSC Arminia Bielefeld da Hoffenheim
  • FC Bayern Munich da VFL Bochum
  • FSV Mainz 05 da SC Fribourg
  • FC Augsburg da Borussia Monchengladbach
  • 1. FC Koln da RB Leipzig

Ranar Lahadi 19 ga watan Satumba

  • VfB Stuttgart da Bayer 04 Leverkusen
  • Borussia Dortmund da FC Union Berlin
  • VfL Wolfsburg da Eintracht Frankfurt