Kasuwar 'yan kwallo: Kane da Tielemans da Martinez da Nandez da Romero da Wijnaldum da kuma Ramsay

Lautaro Martinez
An wallafa

Watakila kyaftin din tawagar Ingila, Harry Kane ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a Tottenham idan a saka masa da kudin da kungiya za ta dauke sho idan wa'adinsa bai kare ba a kunshin kwantiraginsa.

Dan wasan ya ce ya aminta da zama da ya yi da Daniel Levy a bana a lokacin da ya yi shirin komawa Manchester City. (Eurosport)

Dan kwallon tawagar Belgium, Youri Tielemans ya ce kofarsa a bude take don tattaunawa da Leicester City kan saka hannu a sabuwar yarjejenioya, bayan da ake alakanta dan wasan mai shekara 24 da cewar zai koma Liverpoolko Manchester UnitedkoBarcelona ko kuma Real Madrid. (Sky Sports)

Kungiyar Tottenham da kuma Atletico Madrid anki sallama tayin da kowacce ta yi na sama da Yuro miliyan 90 don daukar dan wasan tawagar Argentina, Lautaro Martinez na Inter Milan a bana, wanda Arsenal ta janye jikinta, bayan da ta yi tayi mara tsoka. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Kungiyoyi da dama sun tuntubi dan kwallon tawagar Ingila mai taka leda a Arsenal wato Bukayo Saka, wanda Gunners ta ja kunne da cewar ba za ta sayar da matashin dan wasan ba mai shekara 20. (Here We Go podcast, via Sun)

Kungiyoyi da dama na bibiyar wasan dan kwallon Bayer Leverkusen Florian Wirtz musamman kungiyoyin Premier League har da Bayern Munich. (Express)

Damar Chelseata daukar dan wasanSevilla Jules Kounde za ta dogara ne kan makomar kwantitagin mai tsaron baya Antonio Rudiger a Chelsea idan an karkare ta. (Star)

Arsenal ba ta yanke kaunar daukar dan wasan Lyon Houssem Aouar ba a kakar badi, sai dai Gunners za ta kasa sayen dan kwallon har sai ta samu gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League. (Todofichajes - in Spanish)

Tottenham za ta sake kasancewa cikin wadanda za suyi zawarcin dan wasan Cagliari Nahitan Nandez, wanda Inter Milanda Napolida Romada kuma Fiorentina da zarar an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai a Janairu. (Tuttomercatoweb - in Italian)

Har yanzu Barcelona na son sayen dan kwallon Argentina, Cristian Romero, wanda ya koma Tottenham daga Atalanta a kakar bana. (Fichajes - in Spanish)

Watakila Juventus da kuma AC Milan suyi kokarin rububin daukar dan wasan Real Madrid Isco a watan Janairu. (Calciomercato - in Italian)

Everton na son latsa daukar dan wasan Aberdeen mai tsaron baya fender Calvin Ramsay. An ce Tottenham ta tura wakilai domin kallon rawar da matashin mai shekara 18 zai taka a karshen mako a fafatawa da Motherwell. (Scottish Sun)

Watford na shirin daukar matashin dan wasa mai shekara 18, Jimiel Chikukwa, wanda ya bar Leeds United a kakar tamaula ta bana. (Football Insider)