Manuel Lanzini ya fitar da Man United daga Carabao Cup

Ole Gunner Solkjaer
An wallafa

West Ham United ta dauki fansa a kan Manchester United, wannan karon a Carabao Cup wasan zagaye na uku.

Kungiyar da David Moyes ke jan ragama ta ci Manchester United 1-0 a Old Trafford ranar Laraba.

A minti 9 da fara wasa Manuel Lanzini ya zura kwallo a ragar United, kuma haka aka tashi da ta kai an yi waje da kungiyar Old Trafford a gasar bana.

Ranar Asabar United ta je ta shi West Ham United 2-1 a wasan mako na biyar a gasar Premier League.

A karawar ce Jesse Lingard ya ci kwallo na biyu daf a tashi daga baya kyaftin din West Ham, Mark Noble ya farar da fenariti a cikin karin lokaci.

Shine bugun daga kai sai mai tsaron raga na farko da golan United, David de Gea ya tare, bayan da aka ci shi 40 a jere.

Da wannan sakamakon West Ham ta kai zagaye na hudu a wasan bana, ita kuwa United sai dai ta tara a badi.

United wadda ta yi cefane mai tsada ta fara da rasa kofi daya a bana daga wadanda take fatan lashewa a kakar nan, ciki har da Premier League da FA Cup da Champions League ko kuma Europa League, kafin a kai kofin zakarun nahiyoyin duniya.

Manchster United za ta karbi bakuncin Aston Villa a wasan mako na shida a gasar Premier League ranar Asabar 25 ga watan Satumba.

Ita kuwa West Ham United za ta ziyarci Leeds United ranar Asabar din a dai gasar cin kofin Premier League.