Kasuwar 'yan kwallo: De Ligt da Karius da Martinez da Rudiger da Asensio da kuma Lacazette

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea na son daukar dan kwallon Juventus, mai tsaron baya Matthijs de Ligt, mai shekara 22. (Mirror)
FC Basel na duba yadda za ta dauki golan Liverpool dan kasar Jamus, Loris Karius, mai shekara 28. (Bild - in German)
Barcelona sai ta biya fam miliyan 1.5 ga hukumar kwallon kafa ta Belgium kafin ta samu daukar Roberto Martinez mai shekara 48. (Sport - in Spanish)
Sai dai kuma Martinez ya yi watsi da batun da ake alakanta shi da cewar zai maye gurbin dan kasar Netherlands, Ronald Koeman, wanda ke cikin matsi a Barcelona. (Eurosport)
Bayern Munich na duba halin sayen mai tsaron bayan Chelsea, Antonio Rudiger, sai dai kasar Jamus din na son saka hannu kan tsawaita zamansa a Stamford Bridge. (Bild - in German)
Liverpool na ci gaba da bibiyar matashin dan wasan Real Madrid, Marco Asensio. (Fichajes - in Spanish)
Dan wasan Arsenal, Alexandre Lacazette, ya zaku ya saka hannu kan kwantiragin tsawaita zamansa a Emirates, bayan da yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar bana. (Le10 Sport - in French)
Kocin Chelsea, Thomas Tuchel ya kalubalanci Ruben Loftus-Cheek, da cewar yana son ya gwada masa kwarewar da yake da ita a fagen tamaula, idan yana son ci gaba da zama a kungiyar kafin batun saka shi a wasanni. (Express)
Manchester City ta yi watsi da tayin fam miliyan 15 da Borussia Dortmund ta yi wa Liam Delap. (Football Insider)
Arsenal da kuma AC Milan na son yin zawarcin dan kwallon Club Brugge, Noa Lang. (Express)
Masu daukar 'yan wasa a Barcelona sun kalli rawar da mai tsaron ragar Brighton Carl Rushworth ke takawa wanda yanzu haka ke wasannin aro a Walsall. (Mirror)



























