Kasuwar 'yan kwallo: Bowen da Haaland da Martial da kuma Rudiger

Erling Braut Haaland
An wallafa

Watakila Liverpool ta yi kokarin daukar dan wasan West Ham, Jarrod Bowen a kakar badi. (Liverpool Echo)

Haka kuma watakila Borussia Dortmund ta yi kokarin daukar dan kwallon Juventus Federico Chiesa, domin maye gurbin Erling Braut Haaland ko da zai bar kungiyar a kakar badi. (Calciomercato - in Italian)

Liverpoolta bi sawun masu son zawarcin Erling Braut Haaland batan da babban jami'in kungiar Borussia Dortmund, Hans-Joachim Watzke ya ce zai yi wuya dan kwallon ya ci gaba da taka leda a kungiyar a kakar badi. (Mundo Deportivo, via Mail)

Dan wasan Real Madrid, Marco Asensio yana ckin jerin 'yan wasan da Liverpool ke son dauka. (Fichajes.Net, via Sun)

Dan kwallon Chelsea, Antonio Rudiger,ba zai gaggawar saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da wasa a kungiyar, bayan da zai bukaci a yi masa karin albashi da zai sa ya ci gaba da taka leda a Stamford Bridge. (90min)

Kociyan Bayern Munich, Julian Nagelsmann ya ce bai tattauna ba da daraktan wasannin kungiyar Hasan Salihamidzickan batun Rudiger, wanda yarjejeniyarsa a Chelsea za ta kare a karshen kakar bana. (Eurosport)

Arsenal na shirin rabuwa da Alexandre Lacazette wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar bana, wanda Atletico Madrid ke son daukar dan wasan mai shekara 30. (Le10 Sport, via Mirror)

Manchester United ta tuntubi Barcelona kan ko za ta sayar mata da Ousmane Dembele. (El Nacional, via MEN)