Chelsea v Man City: Wace dabarar ta rage wa Guardiola don kamo Tuchel?

Asalin hoton, Getty Images
Thomas Tuchel ya zama mai horar da 'yan wasa na biyu a duniya da ya taba kara wa da Guardiola sau uku yana doke shi.
Yaya za ku kwatanta shi idan har ya doke Pep sau hudu a jere a haduwar da Manchester City za ta yi da Chelsea?
A lokacin da suke horarwa a Gasar Bundesliga ta Jamus, Tuchel bai taba doke Guardiola ba, amma kamar kar ya zo Chelsea ya doke kociyan na Man City har sau uku a jere gasa daban-daban cikin makonni shida.
Galaba ta karshe da ya samu a kan Guardiola ita ce a wasan karshe na gasar kofin zakarun Turai wadda ta fi kowacce muhimmanci.
Shin me ya kamata Guardiola ya yi a wannan gabar da ya fahimci cewa Tuchel ya zame masa karfen kafa?
Kuma a yanzu da Chelsea ta dare teburi sannan take lokaci, wane irin muhimmanci wasan na ranar Asabar ke da shi ga Pep lura da yadda Tuchel ya shake masa zaiti?
"Abun da kowa ke fadi a City kenan," a cewar tsohon dan wasan Man Cityn, Micheal Brown. Ya kara da cewa "na kalli nasarar da suka yi a kofin Carabao da Wycombe a filin Etihad, kuma abinda yan kallo da tsofaffin yan wasa ke cewa shi ne 'Shin anya Pep na da yadda zai da Chelsea a wasan karshen mako?'
"Hakan ya nuna irin tunanin da a ke yi a kungiyar kansa. Kowa na ganin Pep zai yi rashin nasara ne, kamar dai duk wanda ya yi nasara kansa sai kaga abin ya zama babban labari."
"Shi ne koci daya tilo a duniya da idan aka doke shi kowa sai ya bi diddigin abin da ya sa ya yi rashin nasara komai kankantarsa".
'Koci biyu mafiya dabara'

Asalin hoton, BBC Sport
Har yanzu ba za a ce Tuchel ya kai gagarar da Guadiola ya yi ba, amma kuma idan har ya sake doke ranar Asabar, salonsa zai fara ba da tsoro.
Tun bayan zuwan bajamushen a watan Janairu matsalar da ya samu ba ta taka kara ya karya ba, inda ya lashe kofin zakarun Turai kuma yanzu haka kungiyarsa ke saman teburin Premier League.
Kamar dai Guardiola, shima nasarar da ya ke samu na da alaka da salon wasan da yake amfani da shi.
"Abun da ya fi burge ni da Tuchel ina ganin shi ne yadda ya ke buga salon 3-4-3 a kakar bana, kuma irin wannan salo ne ya yi amfani da shi har Chelsea ta lashe kofin gasar Zakarun Turai bara, a cewar tsohon dan wasan gefen Chelsea kuma mai fashin baki Pat Navin.
"Kuma yanzu kamar ma 3-5-2 suke bugawa ta amfani da Kai Havertz ko Timo Werner yana taimaka wa Romelu Lukaku.
"Kuma ga shi yana da N'Golo Kante da Joginho kum aMateo Kovacic na take musu baya a tsakiya."
"Sannan idan Tuchel ya ga dama zai iya koma wa tsohon tsarinsa na idan yaso ko da a na tsakiyar wasa ne.
"Na yi sa'a na samu damar kallon wasan, don in natsu inga irin salailan da za a yi amfani da su a wannan wasa."
"A wannan iska mai kadawa ba na jin akwai kociyoyi biyu da suka kai Guardiola da Tuchel amfani da kaifin basira wurin sauya salon wasa."
"Amma kuma a yanzu da muke magana salon Tuchel ne yafi na kowa wurin sauya wasa nan take, lura da yadda ya sauya wasan da suka yi da Spurs makon da ya gabata a lokacin da ya shigo da N'Golo Kante bayan dawowa hutun rabin lokaci," in ji Navin.
Me ya dace Guardiola ya yi?
A duka haduwar da Guardiola ya yi da Tuchel a bara ya kan canza salon d aya saba da shi amma kuma bai taba nasara ba.
A wasan kusa da na karshe na kofin kalubale da suka yi Guardiola ya buga 4-3-3, da suka hadu a lig ya buga 3-5-2,.
Sai kuma a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai da suka hadu a Poroto inda ya daba wa kansa wuka da kansa.

Asalin hoton, BBC Sport
A cewar Brown "Chelsea a karkashin Tuchel na gaggawa wurin daukar dama idan suka gano barakar abokin karawa."
A daya waje kuma "Guardiola ya yadda da kansa kuma abune mai kyau don ya yi kokarin mamaye tsakiya ne a wasan karshen," a ra'ayin Navin.
"Saboda haka ya bar lamba hudu ba bu kowa tunanin cewa Ikay Gundogan zai iya aikin amma salon ya ba shi ruwa. Kamar kar Chelsea ta kawo kora sai ga wallen Guardiola ya fito."
"A don haka la'akari da cewa a waje zai tafi wasa ranar Asabar ba makawa zai duba yiyuwar farawa da Fernandinho ko Rodri a lamba hudu."
Masana na ganin cewa ga alama Guardiola zai so ya yi amfani da masu tsaron baya uku, don wasansa ya fi na Chelsea kyau lokacin da ya buga hakan a wasan lig da suka hadu bara.
Amma ba za a iya fahimtar haka ba har sai anga irin zubin nasa da kuma irin sabon salon da ya bijiro da shi a ranar Asabar.
Sai dai ba bu tantama Guardiola zai fito ne da shirin doke Chelsea a gidanta, kuma Thomas Tuchel zai ido sosai ya ga ta inda zai sake toshe shi.



























