Paulo Dybala da Alvaro Morata ba za su buga karawa da Chelsea da Torino ba

Paulo Dybala and Alvaro Morata
An wallafa

'Yan wasan Juventus, Paulo Dybala da Alvaro Morata ba za su buga wa kungiyar wasan da za ta buga da Chelsea da kuma Torino ba.

Kamar yadda koci Massimiliano Allegri ya sanar ranar Lahadi, 'yan kwallon sun ji rauni a fafatawar da Juventus ta yi nasara a kan Sampdoria a gasar Serie A.

Dybala wanda ya ci kwallo a karawar da Juventus da ta doke Sampdoria 3-2 a Turin ya fita daga fili yana kuka a minti 10 da fara wasan, yayin da Morata ya yi rauni a zagaye na biyu.

Wannan babbar koma baya aka samu a Juventus wadda za ta ziyarci Chelsea ranar Laraba a gasar Champions League, bayan nan ta fafata da Torino a wasan hamayya a gasar Serie A ranar Asabar.

Allegri wanda ya ja ragamar wasa na 400 a Serie A a matakin koci ya yi nasara a karo na biyu kenan a Juventus, bayan kasa cin wasa hudu da fara kakar bana.

Karo na 20 a jere da aka zura kwallo biyu a ragar Juventus da ke yin wasa ba tare kwallo bai shiga ragar ta ba tun daga ranar 2 ga watan Maris.