Paris St-Germain da Manchester City: Ana sa ran Messi cikin 'yan wasan PSG

Asalin hoton, Getty Images
Watakila Lionel Messi yana cikin 'yan Paris St-Germain da za su fafata da Manchester City a Champions League ranar Talata, bayan jinya da ya yi.
Kyaftin din Argentina, wanda ya taka leda karkashin Pep Guardiola a Barcelona bai ci kwallo ba har yanzu a wasa uku da ya buga wa sabuwar kungiyarsa, wanda bai yi mata wasa biyu ba, sakamakon jinya da ya yi.
Messi shine kan gaba da ya ci Manchester City kwallaye da yawa - wanda ya zura shida a wasa hudu, har da guda hudun da ya ci City a karawa da Barcelona da biyu a lokacin da kocin yake Bayern Munich.
PSG tana da damar saka 'yan wasanta uku wato Neymar da Kylian Mbappe da kuma Lionel Messi wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or shida jumulla.
City ce ta doke PSG 4-1 gida da waje a wasan daf da karshe a bara, daga baya Chelsea ta lashe kofin a karawar karshe, bayan cin kungiyar Guardiola 1-0.
Tun daga nan PSG ta dauki Messi wanda ya ci kwallo 120 a Champions League da Sergio Ramos, wanda ya lashe kofin Zakarun Turai hudu da golan tawagar Italiya Gianluigi Donnarumma da sauran 'yan wasa da dama.
Tun bayan da Rukunin Abu Dhabi ya fitar da makudan kudi ya sayi City a 2008 da kuma Qatar Sports Investment ya mallaki PSG a 2011, kungiyoyin biyu ke taka rawar gani a fannin tamaula a nahiyar Turai.
PSG ta lashe kofin babbar gasar Faransa bakwai, ita kuwa City ta ci biyar, amma dai sun kasa cin kofin Champions League, bayan da dukkansu suka buga karawar karshe a kaka biyun da ta wuce.
Kungiyoyi biyun za su buga wasannin da kwarin gwiwa, bayan da PSG ke kan teburin Ligue 1 da cin dukkan wasanninta takwas a kakar bana, ita kuwa Manchester City ta je Stamford Bridge ta doke Chelsea a gasar Premier League ranar Asabar.
Sai dai PSG bata ci wasa ba a karawa hudu a Champions League, tun bayan canjaras da Club Bruges a wasan zagayen farko.
City ta casa RB Leipzig 6-3 a gida a wasan farko a cikin rukuni a bana, kuma ta yi karawa 10 ba tare da an doke ta ba a Champions League.
Dan kwallon City, Ilkay Gundogan ba zai buga wasan ba, yayin da Marco Verratti zai koma buga wa PSG tamaula, bayan da bai yi karawa hudu ba, sakamakon jinya da ya yi.



























