'Yan Juventus da za su fafata da Chelsea ran Laraba

Asalin hoton, Getty Images
Juventus ta karbi bakuncin Chelsea a wasa na biyu a cikin rukuni a gasar Champions League ranar Laraba.
Sai dai Chelsea za ta buga karawar ba tare da Mason Mount da Christian Pulisic da N'Golo Kante da kuma Reece James a fafatawar da za su kara a Turin.
Kante ya kamu da cutar korona ya killace kansa, shi kuwa Pulisic da Mount da kuma James na jinya.
Chelsea ta yi rashin nasara a gida da ci 1-0 a hannun Manchester City a gasar Premier League ranar Asabar, karon farko da aka doke ta a kakar bana.
Ita kuwa kungiyar Massimiliano Allegri, Juventus ta yi karawa hhudu ba a doke ta ba, ta kuma koma ta 10 a Serie A, bayan da ta fara kakar bana da kafar hagu.
Chelseata casa Zenit St Petersburg 1-0 a rukuni na takwas, wadda kwallo hudu ne kacal ya shiga ragarta a karawa 14 a Champions League tun fara kakar bara.
Juventus za ta fafata ba tare da tsohon dan kwallon Chelsea, Alvaro Morata da kuma Paulo Dybala.
'Yan wasan Juventus da za su jara da Chelsea:
Masu tsaron raga: Szczesny da Pinsoglio da kuma Perin
Masu tsaron baya: De Sciglio da Chiellini da De Ligt da Cuadrado da Alex Sandro da Bonucci da kuma Rugani
Masu wasa daga tsakiya: Mckennie da Bernardeschi da Chiesa da Rabiot da Locatelli da Bentancur da kuma Kulusevski
Mai cin kwallaye: Moise Keane



























