Watford ta nada Claudio Ranieri sabon kocinta

Leicester City
Bayanan hoto, Ranieri ya lashe kofin Premier a 2015-16 a Leicester City, amma ta raba gari da shi a bana
An wallafa

Kungiyar Watford ta sanar da nada Claudio Ranieri a matsayin sabon kocinta, domin maye gurbin Xisco Munoz wanda ta sallama ranar Lahadi.

Dan kasar Italiya, mai shekara 69 ya koma horar da tamaula a Premier League, bayan rawar da ya taka a Leicester a 2015-16, wanda ya bar Sampdoria tun kan fara kakar bana.

Shine koci na 14 da kungiyar ta dauka tun bayan da iyalan Pozzo suka mallaki kungiyar a 2012.

An umarci Ranieri da ya bunkasa wasannin kungiyar da take yi a Premier League, wadda take ta 14 a kasan teburi, bayan hada maki bakwai a wasa bakwai.

Wasan farko da kocin zai ja ragamar kungiyar shine wanda za ta karbi bakuncin Liverpool ranar Asabar 16 ga watan Oktoba.

Ranieri yana da gogewar da zai iya daga martabar Watford, kungiya ta 21 da ya karbi aikin koci a kaka 35 a horar da tamaula.

Ya lashe kofi takwas a aikinsa na horar da tamaula ciki har da Coppa Italiya tare da Fiorentina a 1995-96 da Super Cup a Valencia a 2004-05 da kuma Premier League da Leicester City ta lashe a 2015-16, karon farko da ta ci a tarihinta.

Ya kuma san laggon gasar Premier League, bayan da ya horar da Leicester City da Fulham da kuma Chelsea.

Raneiri ya kasa tabukawa a Leicester City, wanda ya kai kungiyar daf da 'yan kasan teburin babbar gasar Ingila a lokacin sauran wasa 13 a karkare gasar da ta kai aka sallame shi a 2016-17

Bayan da ya bar Leicester City ya karbi Nantes, sannan ya koma kocin Fulham a 2018, kungiyar da ya yi kwana 106, sannan ta kore shi.

Ranar Lahadi Watford ta raba gari da Munoz, wanda ya yi wata 10 a kungiyar, wanda ya kai Watford gasar Premier League daga Championship a bana.

Dan kasar Sifaniya ya ja ragamar wasansa na karshe a matakin koci ranar Asabar a gasar Premier League da Leeds United ta yi nasara da ci 1-0.