Manchter United ta saka hannun jarin miliyan 9.5 a kasuwa

Manchester United
An wallafa

Masu Manchester United sun saka hannun jarin da ya kai miliyan 9.5 a kasuwa in ji kungiyar da ke buga Premier League.

Hannun jarin ya kai fam miliyan 137.12 da za a yi hada-hada a kasuwar shunku ta New York Stock Exchange.

Wani rahoto da kungiyar ta fitar ta ce ba za ta karbi wani kaso daga hannun jarin da za ta sayar ba.

An sa hannun jarin da sunan darakta Kevin Glazer da kuma Edward Glazer da ya kai kaso takwas cikin 100 na abinda iyalan suka mallaka.

Wannan sanarwar ta zo ne a lokacin da Avram Glazer daya daga iyalan ya sayar da hannun jarin miliyan 70 a cikin watan Maris, kuma United ba ta karbi komai daga hada-hadar da aka yi ba.

Hakan na faruwa ne a lokacin da tsarin kirkirar gasar European Super League bai kai bante ba, wanda United tana kan gaba, wajen kirkirar gasar da aka shirya za ta yi gogayya da ta Zakarun Turai.

Tun farkon shekarar nan United tare da manyan kungiyoyin Turai 11 suka so ficewa daga gasar Zakarun Turai, domin kafa ta su da za su dunga yi a tsakaninsu kishiya ga Champions League.

Shirin bai samu karbuwa ba, bayan da magoya baya da masu ruwa da tsaki da 'yan siyasa da gwamnatoci suka ki amincewa da tsarin.

Hakan ne ya jawo karin rashin jituwa tsakanin magoya bayan United da Iyalan Glazers, wadanda suka mallaki kaso mafi tsoka a kungiyar tun daga 2005.

Tun daga lokacin Iyalan suka yi alkawarin cewar za su dunga tuntubar magoya baya, sannan za su kara sayar da hannun jari da yawa.