Spain ta kawo karshen wasa 37 a jere ba a ci Italia ba

Spain vs Italiya
Bayanan hoto, Rabonda a ci Italiya tun Satumbar 2018 da Portugal ta doke ta 1-0
An wallafa

Tawagar kwallon Sifaniya ta kawo karshen wasa 37 da Italiya ta yi ba tare da an doke ta ba ranar Laraba.

Italiya wadda ke karbar bakuncin wasan Nations League karawar daf da karshe, ta yi rashin nasara da ci 2-1 a gida.

Sifaniya ta ci kwallayenta biyu ta hannun Ferran Torres da ya ci na farko minti 17 da fara wasa, sannan ya kara na biyu kan hutu.

Tawagar Italiya mai rike da Euro 2020, ta farke daya ta hannun Lorenzo Pellegrini, saura minti bakwai a tashi daga wasan na hamayya.

Koda yake Italiya ta kammala karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Leonardo Bonucci jan kati, saura minti uku su je hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon Sifaniya ta kai wasan karshe kenan a Nations Legue na bana, ita kuwa Italiya za ta buga karawar neman mataki na uku ranar Lahadi da duk wadda aka doke tsakanin Belgium ko kuma Faransa da za su buga daf da karshe ranar Alhamis.

Wannan shine karon farko da aka ci Italiya, bayan wasa 37 a jere tun daga 10 ga watan Satumbar 2018 da Portugal ta yi nasara da ci 1-0.

Roberto Mancini ya karbi aikin jan ragamar Italiya cikin watan Mayun 2018, bayan da kasar ta kasa kai wa gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018, wanda Faransa ta lashe.

Bayan da ya fara cin wasa daya da canjaras biyu aka doke shi karo biyu a fafatawa biyar, sai Mancini ya kafa tarihin duniya na buga fafatawa 37 a jere ba tare da an ci Italiya ba, wanda ya yi nasara a karawa 28 da canjaras tara.

Cikin kuma lokacin tawagar ta zazzaga kwallaye 93 aka zura mata 12 a raga kafin wasa da Sifaniya ranar Laraba.

Haka kuma wasa shida ne daga cikin 37 da ta yi a karawar sada zumunta, duk sauran cikin gasa ta fafata har da lashe Euro 2020 a bana.

Wadanda ke kan gaba a tarhin cin wasanni a jere a duniya kan a doke su:

37 — Italiya (2018-2021)

36 — Brazil (1993-1996)

35 — Spaniya (2007-2009)

31 — Argentina (1991-1993)

30 — Faransa (1994-1996), Italy (1935-1939)

29 — Algeria (2018-kawo yanzu)

23 — West Germany (1978-1981), France (2010-2012)