Tyson Fury ya kare kambunsa na WBC a faɗansu da Deontay Wilder

Asalin hoton, Getty Images
Tyson Fury ya yi nasarar kare kambunsa na WBC bayan ya fafata da Deontay Wilder a wasan damben boxing mai cike da ƙayatarwa a filin wasa na T-Mobile da ke Las Vegas na Amurka.
Kusan shekara biyu kenan da Fury ya taɓa doke Wilder, wanda nasarar tasa a yanzu ke nufin ya yi fafatawa 32 kenan ba tare da an doke shi ba - bayan an doke shi sau biyu a zagaye na huɗu a baya.
Fury ya bige abokin hamayayyar tasa a zagaye na uku amma sai Wilder ya miƙe kuma ya saka shi a maƙata har sau biyu a jere.
Wilder ya jure har zuwa zagaye na bakwai amma wasa ya zo ƙarshe a zagaye na 11 lokacin da Fury ya sake bige shi, inda ya kawo ƙarshen ƙalubalen.

Asalin hoton, Getty Images
"An kayar da ni a lokuta daban-daban na wasan, an ji mani ciwo. Wilder ya ƙware wajen kai naushi," a cewar Fury kan abokin faɗan nasa wanda aka kai shi asibiti saboda tsoron abin da ka iya faruwa.
"Faɗa ne mai ƙayatarwa ba wata tantama. Wilder babban dan boxing ne. Kodayaushe nakan ce ni ne gwarzon ɗan boxing na duniya shi kuma na biyu."
Yadda suka bige juna har sau biyar...

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images























