Nations League - Italy ta ddoke Belgium ta yyi ta uku

Nicola Barella
Bayanan hoto, Nicolo Barella ne ya fara ci wa Italia kwallon farko
An wallafa

Italia ta yi nasarar doke Belgium da ci 2-1, ta kuma zama ta uku a gasar Nations League ta bana.

Nicolo Barella ne ya fara ci wa Italia kwallo daga baya Domenico Berardi ya kara na biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga a karawar da suka yi a Turin.

Belgium ta buga kwallo ya bugi turke sau uku, kafin daga baya Charles de Ketelaere ya zare daya, bayan da lokaci ya kure.

Italia ta kawo karawar neman mataki na uku ne, bayan da Sifaniya ta doke ta a karawar daf da karshe, ita kuwa Faransa ce ta yi nasara a kan Belgium a daya wasan na daf da karshe,

Italia ce mai rike da Euro 2020 da ta lashe a bana, ita kuwa Belgium ce ta daya a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon kafa ta duniya.

Idan anjima ne za a buga wasan karshe a Nations League na bana tsakanin Sifaniya da kuma Faransa mai rike da kofin duniya da ta lashe a 2018 a Rasha.