Raphael Varane: Mai tsaron bayan Man Utd ya ji rauni a Nations League

Varane had played the full 90 minutes in his side's Nations League semi-final win over Belgium on Thursday
Bayanan hoto, Varane ya buga wasan daf da karshe da Faransa ta cire Belgium a Nations League ranar Alhamis
An wallafa

Mai tsaron bayan Manchester United, Raphael Varane ya ji rauni a karawar da Faransa ta lashe Nations League ranar Lahadi a Italia.

Mai shekara 38 ya fadi kasa sannan ya rike kafarsa da ta kai Dayot Upamecano ya canje shi saura mintu uku su je hutun rabin lokaci.

Varane ya buga wa Manchester United wasa shida a bana, tuni kuma mai tsaron baya, Harry Maguire ke jinya, wanda bai wa Ole Gunnar Solskjaer wasa da Everton a gasar Premier League ba.

United za ta buga karawar mako na takwas a gasar Premier League da za ta ziyarci Leicester City ranar Asabar.