France ta doke Spain ta zama ta biyu da ta ci Nations League

Kylian Mbappe
Bayanan hoto, Kwallon da Kylian Mbappe ya ci ya bai wa Faransa damar lashe Nations League na bana
An wallafa

Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa kwallon da ta lashe Nations League, bayan doke Sifaniya a Italia ranar Lahadi.

Tawagar Faransa ta yi nasarar doke Sifaniya da ci 2-1 a wasan karshe da suka fafata a Nations League a Italiya.

Sifaniya ce ta fara cin kwallo ta hannun Mikel Oyarzabal daga baya Karim Benzema ya farke wa Faransa.

Mbappe ne ya zura na biyu a raga, bayan da ya buga ta kasan mai tsaron raga, Unai Simon ta fada a raga a fafatawar da suka yi a San Siro.

Faransa ta kawo wasan karshe, bayan da ta doke Belgium a wasan daf da karshe, ita kuwa Sifaniya ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Italia ta kuma taka mata burkin cin wasanni a jere.

Tawagar kwallon kafa ta Portugal ce ta fara lashe Nations League a kakar 2019 a aka fara gudanar da gasar.

Faransa wadda ke rike da kofin duniya da ta lashe a Rasha a 2018 na shirin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi Qatar a 2022.