Colombia 0-0 Brazil: Tawagogin sun raba maki a tsakaninsu

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Brazil ta yi canjaras a karon farko a bana a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ranar Lahadi, bayan da ta tashi 0-0 da Colombia.
Brazil ba ta yi rashin nasara a wasa 12 baya da ta kara da Colombia a fafatawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ba.
To sai dai kuma Colombia ta karbi bakuncin Brazil, bayan wasa shida da ta buga ba tare da rashin nasara ba karkashin koci, Reinaldo Rueda, wadda rabonda ta yi wannan kokarin tun 2008.
Colombia ta taka wa Brazil burki kenan, wadda ta ci wasa tara a jere a karawar neman gurbin zuga gasar da za a yi a Qatar a 2022, wato ta yi wasa 10 kenan ba tare da an doke ta ba.
Da wannan sakamakon Brazil tana mataki na daya da tazarar maki shida tsakaninta da Argentina ta biyu, wadda ta ci Uruguay 3-0 ranar Lahadi.
Ita kuwa Colombia tana ta biyar a kan teburin Kudancin Amurka da maki 15.
Colombia za ta karbi bakuncin Ecuador ranar Lahadi, ita kuwa Brazil za ta kece raini ne da Uruguay ranar Juma'a.
Tawaga hudu ce kan wakilci shiyyar Kudancin Amurka kai tsaye zuwa gasar kofin duniya daga mataki na daya zuwa na hudu, yayin da wadda ta karkare ta biyar kan buga fafatawar cike girbi.



























