Pedri ya amince da kwantiragin ci gaba da wasa a Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta sanar cewar Pedri ya amince da kunshin kwantiragin da ta gabatar masa na tsawaita zamansa a kungiyar.
Tuni kuma ta ce ta gindaya Yuro biliyan daya ga duk kungiyar da ke son daukar dan wasan idan kwantiraginsa bai kare a Nou Camp ba.
Yanzu kenan yarjejeniyarsa za ta kare a Barcelona ranar 30 ga watan Yunin 2026, ana kuma sa ran zai rattaba hannu ranar Juma'a.
Pedri ya koma Nou Camp da taka leda daga Las Palmas cikin watan Agustan 2020, wanda ya yi wasa 53 a kakar bara a kungiyar - shine kan gaba a yawan buga wata wasanni a kakar da wuce.
Kocin Sifaniya, Luis Enrique ya fara wasa da shi a dukkan karawar da tawagar ta yi a gasar ta nahiyar Turai da Italiya ta lashe.
Matashin dan wasan ya taimaka wa Sifaniya ta ci lambar azurfa a gasar Olympic, bayan da suka yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Brazil.
Pedri ya buga wa Barcelona wasa hudu a bana, wadda ke fama da kalubale, wadda take ta bakwai a teburin La Liga.
Haka kuma kungiyar tana ta karshe a teburin Champions League, bayan da aka doke ta wasa biyu a jere a bana.



























