Raheem Sterling: Dan kwallon Man City zai iya koma wa murza leda a kasar waje

Raheem Sterling
Bayanan hoto, Raheem Sterling ya soma cin benci a Man City
An wallafa

Dan kwallon gaba na Manchester City Raheem Sterling ya ce zai iya koma wa kasar waje domin murza leda idan har ba a ba shi dama sosai a Etihad.

Dan wasan Ingila din wanda kwangilarsa za ta kare a shekara ta 2023, ya ce "ina yaro na yi mafarkin buga kwallo a kasar waje".

"Idan akwai dama a wata kasar, to a shirye nake," in ji Sterling mai shekaru 26.

Wasa daya tal aka soma da Sterling a gasar firemiya ta bana duk da cewa ya buga wasan Gasar Zakarun Turai inda suka sha kashi a hannun Paris St-Germain.

Tun komawar Jack Grealish daga Aston Villa a kan fan miliyan 100 aka soma tababa a kan makomar Sterling a City.

Sterling ya koma City ne Liverpool a shekarar 2015 kuma ya lashe gasar firemiya sau uku da kofin FA sau daya da kuma na EFL sau hudu.