Leicester 4-2 Manchester United: Leicester City ta karya lagon Manchester United

Yadda Leicester City ta casa Manchester United
Bayanan hoto, Yadda Vardy ya ci ragar Manchester United
An wallafa

Leicester City ta casa Manchester United ci 4-2 a fafatawar da suka yi a King Power gidan Leicester.

Kwallaye biyu da Leicester ta ci ana dab da hure wasa suka taiamaka ta samu nasara kan Manchester United.

Wannan ya kawo ƙarshen wasa 29 da Manchester United ta buga a waje ba a doke ta ba.

Marcus Rashford da aka sako daga baya ya yi ƙoƙarin farkewa Manchester United ƙwallo ta biyu amma bayan kusan minti ɗaya Vardy ya sake zura wa Leicester City ƙwallo ta uku.

Daga baya Patson Daka ya ƙara ƙwallo ta huɗu ana dab da hure wasan.

Mason Greenwood ne ya fara ci wa United ƙwallo amma Leicester ta farke.

A ɗaya ɓangaren Manchester city ta doke Burnley ne ci 2-0 a Etihad, inda City yanzu ta dawo matsayi na biyu saman teburin Premier.

Liverpool ta doke Watford 5-0, yayin da Chelsea ta samu sa'ar Brentford 1-0.

Chelsea ce saman tebur da maki 19, Liverpool ce ta biyu da maki 18, yayin da Manchester ke matsayi na uku da maki 17.

Manchester United ta koma matsayi na biyar da maki 14 bayan ta sha kashi hannun Leicester City.