Barcelona za ta karbi bakuncin Valencia a La Liga ranar Lahadi

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Valencia ta ziyarci Barcelona, domin buga wasan mako na tara a gasar La Liga ranar Lahadi.
Valencia tana mataki na takwas a kan teburin La Liga da maki 12, iri daya da na Barcelona mai kwantan wasa daya, wadda take ta tara a kan teburin.
Kungiyoyin biyu sun kara a bara a La Liga, inda suka tashi 2-2 ranar 19 ga watan Disambar 2020 a Nou Camp, yayin da Barcelona ta je ta ci Valencia 3-2 a wasa na biyu ranar 2 ga watan Mayun 2021.
Ronald Koeman ya ce watakila Sergio Aguero ya fara buga wa Barcelona wasa ranar Lahadi, karon farko da zai buga mata gasa kenan.
Dan kwallon tawagar Argentina, ya koma Sifaniya daga Manchester City a bana, bayan da kwantiraginsa ya kare a Manchester City a watan Yuni.
Wannan karawar za ta zama kalubale ga kungiyoyin biyu da kuma Ronald Koeman, wanda zai karbi bakuncin Dynamo Kiev ranar Laraba a Nou Camp a Champions League.
Daga nan kuma Barcelona ta kara da Real Madrid a wasan hamayya na El Clasico a gasar La Liga ranar Lahadi.
Shima Ansu Fati watakila za a iya fara karawar da shi a karon farko tun bayan da ya ji rauni a Nuwambar bara.
Sai dai kuma Barcelona za ta buga wasan ba tare da Ronald Araujo da Pedri da kuma Martin Braithwaite ba a fafatawar ta ranar Lahadi da Valencia.
Karon farko da Barcelona za ta buga wasan da aka amince 'yan kallo su cika Camp Nou, wadda rabon da hakan ta faru tun bayan Maris din 2020, sakamakon bullar cutar korona.
Wasannin mako na tara da za a buga ranar Lahadi:
- Rayo Vallecano da Elche
- Celta Vigo da Sevilla
- Villarreal da Osasuna
- FC Barcelona da Valencia C.F



























