Srgio Aguero yana cikin 'yan wasan Barcelona da za su kara da Valencia

Asalin hoton, Getty Images
Sergio Aguero yana cikin 'yan wasan da za su fafata da Valencia a gasar La Liga a Camp Nou ranar Lahadi.
Karon farko da dan kwallon tawagar Argentina zai fara taka leda a Barcelona tun bayan da kwantiraginsa ya kare a Manchester City cikin watan Yuni ya koma Sofaniya.
Aguero wanda yana cikin 'yan wasan da ya taimakawa Argentina ta lashe Copa America a bana, ya ji rauni tun kan fara kakar bana da ta kai ya yi jinya.
Ana sa ran Ronald Koeman ka iya fara wasan na Valencia da shi ko kuma ya canji dan wasa.
'Yan wasan na Barcelona: Ter Stegen da Dest da Pique da Sergio da Riqui Puig da Memphis da Ansu Fati da Demir da Neto da Coutinho da Lenglet da L. De Jong da kuma Jordi Alba.
Sauran sun hada da Kun Aguero da S . Roberto da F. De Jong da O. Mingueza da Umtiti da Eric da Inaki Pena da Nico da Gavi da kuma Balde.
Wadanda ke jinya: Araujo da Pedri da Braithwaite da kuma Dembele.
Valencia tana mataki na takwas a kan teburin La Liga da maki 12, iri daya da na Barcelona mai kwantan wasa daya, wadda take ta tara a kan teburin.
Kungiyoyin biyu sun kara a bara a La Liga, inda suka tashi 2-2 ranar 19 ga watan Disambar 2020 a Nou Camp, yayin da Barcelona ta je ta ci Valencia 3-2 a wasa na biyu ranar 2 ga watan Mayun 2021.



























