Barcelona 3-1 Valencia: Sergio Aguero ya fara yi wa Barac tamaula

Asalin hoton, Getty Images
Sergio Aguero ya fara buga wa Barcelona tamaula a karon farko ranar Lahadi, tun bayan da ya koma kungiyar daga Manchester City a bana.
Barcelona ta yi nasarar doke Valencia da ci 3-1 a wasan mako na tara da suka kara a Camp Nou a gasar ta La Liga.
Aguero ya koma Sifaniya da taka leda, bayan da kwantitaginsa ya kare a Etihad a karshen watan Yuni, wanda ya ji rauni tun kan fara kakar bana.
Ya kuma shiga karawar sauran minti uku a tashi daga wasan, bayan da Philippe Coutinho ya ci na uku, kuma na farko a kungiyar tun bayan kusan wata 11.
Ansu Fati ne ya farke kwallon da Valencia ta fara ci ta hannun Jose Gaya a minti biyar da take leda, kuma ta farko da Ansu Fati ya ci tun bayan kusan shekara daya, bayan jinya da ya yi.
Barcelona ta zura kwallo na biyu a raga ta hannun Memphis Depay a bugun daga kai sai mai tsaron raga..
Rabon da Coutinho ya ci wa Barcelona kwallo tun wadda ya ci a wasan da kungiyar Camp Nou ta ci Osasuna 4-0 cikin watan Nuwambar 2020.
Da wannan sakamakon, Barcelona ta hada maki 15 tana ta bakwai a teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Rea Madrid ta biyu da kuma tazarar maki biyar tsakaninta da Real Sociedad mai jan ragama.
Barcelona mai kwantan wasa a babbar gasar Sifaniya za ta buga wasa na uuku na cikin rukuni a Champions League ranar Laraba.



























