Abin da ya kamata ku sani kan wasan Arsenal da Palace

Asalin hoton, Getty Images/BBC
Arsenal za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan mako na takwas a gasar Premier ranar Litinin.
Gunners tana mataki na 13 a teburin Premier da maki 13, ita kuwa Palace itace ta 14 mai maki bakwai.
Kungiyoyin sun fafata a kakar 2020/21, inda suka tashi 0-0 a gasar Premier ranar 14 ga watan Janairun 2021, a wasa na biyu kuwa Arsenal ce ta je ta ci Palace 3-1 ranar 19 ga watan Mayun 2021.
Wannan shine karon farko da Patrick Viera zai je Emirates a matakin kocin Palace, wadda ta dauki tsohon kyaftin din Gunners a bana.
Arsenal ta yi rashin nasara a wasa daya tal daga takwas baya da ta fafata da Palace, wadda ta ci uku da canjaras hudu.
Sai dai kuma ta kasa cin wasa a karo uku bayan nan da ta karbi bakuncin Palace, wadda ta yi nasara a daya da canjaras biyu a Emirates.
Palace ta yi nasara ne a karawa hudu daga wasa 42 da suka kara a Lik da Arsenal da suka yi canjaras 13 aka doke ta 25.
Kwazon Arsenal a bana:
Ba a doke Arsenal a wasa hudu a Premier da cin karawa uku da canjaras daya, kuma kwallo bai shiga ragarta ba a wasa uku.
Sai dai kwallo biyar Gunners ta zura a raga a karawa bakwai, kakar da ta ci karancin kwallaye kenan tun bayan 1986-87.
Arsenal ta sha kashi a wasa hudu daga 14 da ta buga a gida a Premier League a 2021 - wannn ce shekarar da ta kasa kokari a gida tun bayan da aka doke ta shida a 1997.
Arsenal ta yi nasara a wasa bakwai da ta fafata a Premier League a gida ranar Litinin da cin kwallo 15 aka zura mata biyu kacal a raga.
Pierre-Emerick Aubameyang ya zura kwallo bakwai a raga a karawa takwas a Premier League ranar Litinin.
Kokarin Crystal Palace a kakar nan:
Wasa daya Crystal Palace ta yi rashin nasara a karawa shida a Premier League da cin daya da canjaras hudu.
Sai dai kuma wasa daya ta ci a fafatawa tara da ta buga a waje da canjaras biyu aka doke ta karawa shida.
Kwallo daya tal Palace ta ci a minti 45 din farko a bana - ba wata kungiya da ta kasa bajintar Palace a Premier League kan hutu.
Kwallo hudu daga biyar da Palace ta ci a bana, yan wasan da suka shiga karawar daga baya, wato masu canji ne suka ci su.



























