Atletico Madrid 2-3 Liverpool: Salah ya ci kwallo

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta ci wasa na uku a karawa uku a rukuni na biyu, bayan da ta je ta doke Atletico 3-2 ranar Talata.
Liverpool ta ziyarci Sifaniya a wasa na uku-uku cikin rukuni a gasar Champions League da suka fafata.
Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Mohamed Salah minti takwas da fara wasan, sannan Naby Keita ya kara na biyu minti biyar tsakani.
Atletico Madrid a farke kwallo biyun ta hannun Antoine Griezmann, wanda daga baya a ka bai wa jan kati ya fita daga fafatawar.
Liverpool ta zura kwallo na uku ta hannun Salah a bugun daga kai sai mai tsaron raga, wanda ya buga ya ci.
Kungiyoyin biyu sun kara a gasar Zakarun Turai sau bakwai kenan, inda Atletico ta yi nasara a karawa uku da canjaras biyu, Liverpool ta ci wasa biyu kenan.
Wasa shida da aka kara tsakanin Liverpool da Atletico:
Kakar 2021/22 Champions League
Ranar Talata 19 ga watan Oktoba
- Atletico 2-3 Liverpool
Kakar 2008/09 Champions League
Ranar Laraba 22 ga watan Oktoban 2008
- Atl Madrid 1 - 1 Liverpool
Ranar Talata 4 ga watan Nuwambar 2008
- Liverpool 1 - 1 Atl Madrid
Kakar 2009/10 Europa League
Ranar Alhamis 22 ga watan Afirilun 2010
- Atl Madrid 1 - 0 Liverpool
Ranar Alhamis 29 ga watan Afirilun 2010
- Liverpool 2 - 1 Atl Madrid
Kakar 2019/20 Champions League
Ranar Talata 18 ga watan Fabrairun 2020
- Atl Madrid 1 - 0 Liverpool
Ranar Laraba 11 ga watan Mayun 2020
- Liverpool 2 - 3 Atl Madrid
Liverpool ta buga karawar tare da Alisson Becker da kuma Fabinho, wadanda ba su yi mata wasan Premier League da ta doke Watford da ci 5-0 a ranar Asabar ba.
'Yan wasan biyu sun je Spaniya kai tsaye, bayan buga wa tawagar Brazil wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Haka kuma Liverpool ba ta je Sifaniya da Curtis Jones ba, wanda bai yi mata fafatawa da Watford ba, sakamakon jinya da yake yi.
Shima Thiago Alcantara na jinya, wanda bai buga wa Liverpool wasa biyar kenan kawo yanzu.
Haka kuma Roberto Firmino wanda ya ci kwallo uku rigis a Premier League ranar Asabar, ya buga wa Liverpool karawa ta 300 a kungiyar a dukkan fafatawa.
Liverpool ta ci gaba da zama ta daya da maki tara a rukuni na biyu, sai Atletico ta biyu da maki hudu da kuma FC Porto mai maki hudu da Milan ta karshe a teburin, wadda ba ta da maki.
Sakamakon wasannin Champions League da aka buga ranar Talata:
- Club Brugge 1-5 Manchester City
- Besiktas 1-4 Sporting C
- Inter Milan 3-1 FC Sheriff Tiraspol
- Ajax Amsterdam 4-0 Borussia Dortmund
- Atletico Madrid 2-3 Liverpool
- Paris Saint-Germain 3-2 RB Leipzig
- FC Porto 1-0 AC Milan
- Shakhtar Donetsk0-5 Real Madrid



























