Paris St-Germain 3-2 RB Leipzig: Lionel Messi ya ci kwallo biyu

Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi ya ci wa Paris St-Germain kwallo biyu a karawar da ta doke RB Leipzig 3-2 a Champions League ranar Talata.
Kylian Mbappe ne ya fara ci wa PSG kwallo a wasa na uku-uku na cikin rukuni da suka kara a Faransa.
Sai dai kuma Andre Silva ne ya farke kwallon, sannan Nordi Mukiele ya kara na biyu da kungiyar Jamus ta shiga gaba.
Daga baya ne Messi ya farke wa PSG, sannan ya ci na uku a bugun fenariti.
PSG ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga daf da za a tashi, maimakon Messi ya karbi kwallon ya buga, sai Mbappe ne ya karba ya buga kwallo ya yi sama.
Kungiyar Faransa tana saman Manchester City a rukunin farko da maki bakwai a Champions League.
Kawo yanzu Messi ya ci kwallo uku a PSG a Champions League, tun bayan da ya koma kungiyar, wanda ya ci daya a wasan da suka doke Manchester City 2-0.
Messi tsohon dan kwallon Barcelona ya ci kwallo 123 a gasar Zakarun Turai kenan da 120 da ya zura a raga a Barcelona, kuma Leipzig itace ta 37 da ya ci a Champions League.
Kyaftin din Argentina ya zama na hudu da ya zura kwallo a wasa biyu a jere a PSG da komawarsa kungiayar da taka leda, bayan Neymar da Alex da kuma George Weah.
Kawo yanzu Leipzig ta yi rashin nasara a wasa uku a Champions League a bana, kuma wasa hudu ta ci a bana a dukkan fafatawa tun bayan da Jesse Marsch ya karbi aikin horar da kungiyar.



























